MAS’LAHA TSAKANIN MUSULMI DA HAKKIN MUSULMI AKAN MUSULMI Fitowa ta 001 1.SALLAMA: Anaso a Kan sunnah duk lokacin da musulmi ya hadu da Dan uwansa musulmi yayi masa sallama gabanin yin wadansu magangannu. Sallamar zata kasance Kamar haka:-“ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLH “Sa’annan Kuma ya bashi Hannu suyi musafaha. Shi Kuma dayan Sai ya amsa Yana Mai cewa:wa’alaikumussalamu warahamatullh wabarakatuhu”. Wanannan yazama saboda fadar ubangiji Allah(SWT) a cikin Al-kur’ani sa Mai girma :”Kuma Idan an gaisheku da wata gaisuwa, ku amsa gaisuwar da abin da Yake mafi kyau daga Gare ku ko Kuma ku mayar da ita”(4:86)abinda nufi anan shi ne kada ka nakkasa ma Dan uwanka Koda ga gaisuwa ce. Hakanan Kuma fadar annabi (SAW) “kuji tsoron Allah duk Wanda ke tafiya Akan wani Abu yayi sallama ga Mai tafiya a kasa yayi da suka hadu.maitafiya a kasa shi my zai yi sallama ga Wanda ke zaune.jama’a kadan a lokacin da zata iske jama’a masu Yawa zasu yi musu sallama.” Annabi (SAW) yaci gaba da cewa “mala’ikku suna ta’ajibin musulmi da zai hadu da Dan uwansa musulmi ya kasa yi masa sallama”. Ya Kuma ci gaba da cewa musulmi yayi sallama ga Wanda ya Sani da Kuma Wanda Bai Sani ba.hakanan Kuma Annabi (SAW) yana cewa musulmi biyu basu haduba suna yin sallama da musafaha da Juna face Sai Allah (SWT) ya gafarta musu gabanin su rabu. Haka Nan Kuma Annabi (SAW)yayi muna umurni da kada mu amsa ma mutumin da ya sadu da mu yayi muna magana kafin yayi muna sallama Daga Dan uwanku Abubakar Rabiu Yari 28/07/1437 05/05/2016
Advertisements