Izala tayi kira ga ‘yan social media da su Kara jajircewa akan yin aiki domin Allah, Musamman a wannan wata ta Ramadan. Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau shine jagoran Kungiyar a tarayyar Naijeriya, shi ya yi wannan kira na musamman ga masu aiki da social media da su kara jajircewa akan yin aiki domin Allah. Shugaban yayi wannan kiran ne a lokacin da yake bada umurni ga shugaban Jibwis Social Media ta Naijeriya Ibrahim Baba Suleiman, na yadda za’a tsarkake wannan kafa ta yanar gizo, ya zama ya’da Da’awa yafi komi muhimmanci a wannan kafa, maimakon ayi ta soki burutsu ko wani abun da baida amfani sabanin wannan. “Ku ‘yada Alkhairi domin shi kuke da shi” Inji shi. Shuganan yace ‘Yan Social Media su zama jakadun Musulunci a wannan kafa, Musamman a wannan wata na Ramadan da yake gaban mu, lura da ayyukan alkhairi suna da yawa a wannan wata, akwai ya’da Tafsirai, Hudubobi, Tallafawa marayu, da sauran ayyukan da ake gabatarwa, wanda Social Media tana da rawar da zata taka a wannan bangare insha Allah. Daga karshe shugaban ya nemi Shugabannin Jibwis na jihohi da sauran matakai da su baiwa yan Kwamitin goyon baya domin samun saukin tafiyar da ayyukan nasu. A lokacun maida Bayanin sa, Shugaban Jibwis Social Media na kasa, Ibrahim Baba Suleiman ya yi godiya da wannan kira da shugaba yayi, ya kuma ce Kwamitin nasu sun shirya tsaf domin sanar da zunzurutun miliyoyin mabiya halin da ko wane Malami yake ciki, kama daga Kasar Naijeriya da sauran kasashen Afirka inda Kungiya ta tura Malamai domin gabatar da Tafsirin Al-qurani mai girma a wannan wata mai daraja da ikon Allah. Jibwis Nigeria 28/Sha’aban/1437 04/June/2016
Advertisements