FATAWAR RABON GADO (34)
Advertisements
Tambaya:
Assalamu alaikum warahmatullah Dr. Dan Allah zan iya yin wasiyya ga kanina ya hakura da gadona dan mata ta tayi amfani da shi, Domin na san kanin ba zai kula da Matar tawa ba Idan na mutu?.
Amsa:
Wa alaikum assalam, wanda za’a gada ba shi da ikon hana magajinsa gado.
Allah madaukakin sarki shi ne ya dauki nauyin raba gado ga wadanda suka can canta da kansa,ya kuma yi alkawarin narkon wuta ga dukkan wanda ya sabawa dokokin da ya sa na rabon gado a aya ta: 14 a suratun Nisa’i.
Mutukar kaninsa yana cikin magada ba shi da ikon hana shi, ko da ya yi wasiyya, ya wajaba alkali ya bata ta.
Dukiya tana zama mallakin magada daga zaran an tabbatar da mutuwar mamaci.
Idan har kanin naka ya sarayar da hakkinsa da kansa, to babu laifi tun da damarsa ce.
Allah ne mafi sani.
Amsawa: Dr jamilu Zarewa.