FATAWAR RABON GADO (38)
Advertisements
Tanbaya.
Ina da tambaya kan KALALA.
Idan mutum ya rasu, bashi da mata, ba d’a ba uba.
Amma yana da ‘yan uwa SHAQIQAI maza da mata DA LI’ABBAI maza da mata.
Yaya gadon sa zai kasance?.
Amsa:
Wa’alaykumussalam. In har maza da mata ne shakikan, sune zasu gaje dukiyar duka, kowanne namiji a cikinsu a bashi rabon mata biyu.
‘ yan uba basayin gado mutukar akwai namiji a shakikai.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa
26/07/2016