Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home ยป IDAN MAMACI BA SHI DA YA'YA ,ZAI IYA WASIYYA DA DUKKAN DUKIYARSA
FATAWA

IDAN MAMACI BA SHI DA YA'YA ,ZAI IYA WASIYYA DA DUKKAN DUKIYARSA

iGeekBy iGeekJuly 28, 2016No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

IDAN MAMACI BA SHI DA ‘YA’YA, ZAI IYA WASIYYA DA DUKKAN DUKIYARSA ?

Advertisements

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Da Allah malam Ina da tambaya kamar haka: shin saurayin da bai yi aure ba, amma yana da iyaye da ‘yan’uwa a raye, zai iya yin wasiyya da rabin dukiyar shi, kasancewar  ba shi da ‘ya’ya ?  Nagde

Amsa:

A zahirin hadisai ingantattu har wanda ba shi da ‘ya’ya ba zai yi wasici da sama da daya daga cikin uku na dukiyarsa ba, saboda Annabi s.a.w yana cewa da Sahabinsa Sa’ad (RA) lokacin da ya so ya yi wasiyya da mafi yawan dukiyarsa: “Ka bar magadanka cikin wadata, ya fi ka bar su matalauta suna rokon mutane”.                                                              
Kasancewar Annabi (S.a.w) ya yi amfani da lafazin magada, hakan sai ya nuna ko ba ‘ya’ya ba za’a yi wasiyya da sama da daya cikin uku na dukiya ba, saboda hakan zai cutar da ragowar magada, ya iya jefa su cikin talauci bayan mutuwar magajinsu.                           

Aya ta: 12 a cikin suratu Annisa’i tana nuna cewa: Wanda zai mutu ba shi da ‘ya’ya, ba shi da iyaye, ba zai yi wasiyya da abin da zai cuci magadansa ba.

Allah ne mafi sani.

Amsawa: Dr Jamilu zarewa.

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Yawun Bakin Budurwa Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

March 12, 2018

Khudubar Ranar Juma'a Mai taken Sulhu Alheri ne Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

February 18, 2018

[Audio] Download Raddi Mai Taken 'Babban Bola' ? Sheikh Bello Yabo Sokoto

July 24, 2017
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.