MACE ZA TA IYA YIN ALKALANCI ?
Advertisements
Tanbaya :
Assalamun alaykum Warahmatullahi wabarakatuhu bayan sallama irin ta musulunci malam inayi maka fatan alheri Allah yasa kana cikin koshin lafiya.
Tanbayata malam ya halatta mace ta yi alkalanci a musulunci,
Allah yakarawa malam lafiya.
Amsa:
Wa alaikum assalam, a wajan mafi yawan malamai mace bai halatta ta yi alkalanci ba, saboda hadisin Abu-bakrata wanda Annabi s.aw. yake cewa: “Duk mutanen da suka jibintawa mace lamuransu ba za su rabauta ba” kamar Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4425. Alkalanci yana bukatar nutsuwa da daidaiton yanayi, wannan yasa Annabi s.a.w. ya hana wanda yake cikin fushi ya yi alkalanci, kamar yadda Muslum ya rawaito, mace kuma idan ta fara jinin haila takan fita daga daidaito, ta yi abin da bai dace ba, wannan yake nuna rashin dacewarta da wannan aiki na Annabawa da manzanni.
Allah ne mafi sani.
13/07/2016
DR Jamilu Yusuf Zarewa