MIJINA YA SADU DA NI TA DUBURA CIKIN KUSKURE ?
Advertisements
Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakaatuhu :
Miji ne ya je saduwa da matar sa sai ya kuskure ya saka mata a dubura shin mene ne hukuncinsa?
Amsa:
Wa alaikumus salam wa rahamatullahi wa barakaatuhu, In har da kuskure ya saka mata a dubura, sai ya yi maza ya zare, mutukar ya cire daga zarar ya ji ba wurin ba ne Allah ba zai kama shi da laifin hakan ba. A karshen suratul Bakara “Ya ubangijinmu kar ka ka kamamu in mun manta ko mun yi kuskure” Muslim ya rawaito hadisi cewa: Allah ya zartar da hakan. Ibnu-majah ya rawaito hadisi, Annabi s.a.w. yana cewa: “Allah ya yafewa al’umata abin da suka aikata cikin kuskure”. Cigaba da jin dadi a wurin bayan gano kuskuren, yana daga cikin zunubai.
Allah ne mafi sani
Dr Jamilu Yusuf Zarewa
11 Shawwal, 1437 (16/07/2016).