WANDA YA SHA RUWA DA MANTUWA A AZUMIN NAFILA, AZUMINSA YAYI?
Advertisements
Tanbaya :
Assalamu Alaikum! Malam barka da war- haka.. Tambayace dani, qanwata ce tana azumin sitta shawwal sai tai mantuwa taci abu… Wasu sun ce wai axuminta ya karye tunda nafila ne. Shin hakan da suka fada gaskiya ne?
Amsa :
Wa alaikum assalam, Wanda yake azumi ya manta ya ci abinci ko ya sha abin sha, Allah ne ya ciyar da shi kuma ya shayar da shi, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisi, don haka azuminsa ya yi, babu banbanci tsakanin azumin nafila da na farilla.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
9 Shawwal 1437.
15/07/2016.