Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home » ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI ?
FATAWA

ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI ?

iGeekBy iGeekAugust 24, 2016No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
ZAN IYA YIWA MAMACI AIKIN HAJJI ?
Tambaya:
Assalamu alaikum wa rahmatullah, Malam Barka da dare, Malam ina tambaya ne dangane da wakilci a aikin hajji (Anniyaabatu anil mayyit), mahaifina yana son yiwa wani daga cikin makusantan shi da ya rasu; sai wani mutum (malami) yake ce masa ai akwai addu’ar da ake yi (qul huwal laahu sau wani adadi dss) wadda tafi wannan aikin hajjin da za ai masa!!
To dan Allah Malam yana so ne yaji shin hakan ya tabbata, kuma dai-dai ne? , ko akwai wani Malami da ya fadi hakan?
Amsa:
Wa alaikum assalam,Ba haka ba ne, wannan maganar ba ta da asali, Yiwa wani hajji ya tabbata a hadisai, wani mutum ya tambayi Annabi (s.a.w) cewa: “Babana ya mutu bai yi hajj ba, zan iya yi masa?, sai Annabi (s.a.w) ya ce yaya kake gani Idan da bashi ya bari za ka biya masa?,sai yace E,sai Annabi (s.a.w) yace to ai bashin Allah shi ya fi cancanta a biya, don haka ka yi masa hajji, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya rawaito a Muntaka a hadisi mai lamba ta: 1797, da kuma Darakudni.
Sannan Kathamiyya ta tambayi a Annabi (s.a.w) cewa : Hajji ya riski babanta yana tsoho za ta iya yi masa? sai Ya ce E, kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta ; 1756.
Malaman fiqhu sun kafa hujja da Wadannan hadisan tabbatattu akan halacci ko wajabcin yiwa mamaci ko Wanda ba zai iya ba aikin hajji Idan yana da halı.
Hajji ibada ce mai zaman kanta,kuma daya daga cikin ginshikan musulunci babu yadda za’a yi wata addu’a ta zauna a makwafinta.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
2942016
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Yawun Bakin Budurwa Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

March 12, 2018

Khudubar Ranar Juma'a Mai taken Sulhu Alheri ne Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

February 18, 2018

[Audio] Download Raddi Mai Taken 'Babban Bola' ? Sheikh Bello Yabo Sokoto

July 24, 2017
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.