ZAN IYA RIKE HANNUN BUDURWATA?
Tambaya:
Malam Ya Hukunchin Wanda ya rike Hannun wata mace Kuma ba matarsa ba ce, amma Budurwarsa ce?
Amsa:
Wa alaikumus salam, Bai hallata mutum ya rike hannun wacce ba muharramarsa ba, kuma ba matarsa ta aure ba. Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance ba ya Musafaha (hada hannu) da mata yayin da zai musu mubaya’a, yana yi musu mubaya’a ne da Magana, kamar yadda ya tabbata a hadisi.
Taba hannun budurwa hanya ce da take kaiwa zuwa ga Zina saboda yana tayar da sha’awa, Allah Madaukaki ya haramta kusantar zina a aya ta 32 a suratul Isra’i, Zina tana daga cikin manyan zunuban da babu kamar su bayan shirka da Allah.
Wanda ya kiyaye dokokin Allah, tabbas Allah zai kiyaye shi, wanda ya bı son zuciyarsa, to Allah yana nan a madakata.
Allah ne mafi sani.
Dr Jamilu Zarewa.
05/05/2016.