AZUMI GOMA A FARKON ZUL-HIJJA ?
Tambaya:
Assalam alaikum Dan Allah mlm menene ingancin azumi Guda goma da ake awatan zulhijja?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Hadisi ya tabbata a Sunan Annasa’i: Annabi (s.a.w) ya kasan ce yana azumtar kwanaki Tara na farkon Zul-hijja.
Ba’a azumtar rana ta goma saboda ita ce ranar sallah, Annabi (s.a.w) ya haramta azumtar ranar sallah a hadisin da babban sahabi Umar ya rawaito.
Allah ne mafi sani
Allah ne mafi sani
Amsawa: Dr Jamilu Zarewa.
3/8/201
3/8/201