FATAWAR RABON GADO (51)
Tambaya:
Mutum ne ya rasu ga wadanda ya bari a duniya: Matarsa1, yar’sa guda 1 mace,sai ‘ya’yan kanin sa maza 3 mata 2,sai kuma ‘ya’yan yayar shi mace da namiji.?
Amsa:
Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida: 8, a bawa matarsa kashi daya, ‘yarsa kashi hudu, ragowar kashi ukun sai a bawa ‘ya’yan kaninsa Maza in shakiki ne ko li’abbi.
‘Ya’yan dan’uwan da aka hada uwa daya kawai ba sa gado, haka ‘ya’yan ‘yan’uwa Mata.
‘Ya’yan dan’uwan da aka hada uwa daya kawai ba sa gado, haka ‘ya’yan ‘yan’uwa Mata.
Allah ne mafi sani.
Dr jamilu Zarewa 31/8/2016