DAGA YANZU MAHAJJATAN NIGERIA BA ZA SU SAKE HALARTAR JIFAN SHAIDAN BA ! ! !
Tambaya:
Dr muna so ayi mana bincike akan wannan : Daga Yanzu Mahajjatan Nijeriya Ba za Su Sake Halartar Jifan Shedan Ba, Inji Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II kuma Amirul Hajji na bara, a hajjin da ya gabata ya bayyana cewa daga yanzu mahajjatan Nijeriya ba za su sake halartar jifan Shedan ba, saidai idan an sama musu masauki a kusa da Jamrat inda a nan ne za a gudanar da jifan, Ya kuma kara da cewa bakaken fata irin al’ummar Nijeriya bai zama wajibi sai sun gudanar da jifan Shedan ba.
Sarkin ya bayyana hakan ne bayan yawan mace-macen da aka samu a wurin turmutsitsin jifan Shedan a hajjin bara, wanda ciki har da mahajjatan Nijeriya kimanin saba’in suka rasa ransu. Ya kuma kawo hujjoji da dama daga ayoyin Kur’ani, wadanda suka nuna cewa rashin halartar jifan Shedan ba zai kawo rauni a hajjin mahajjaci baa .
Amsa:
Ina rokon Allah ya ba mu dacewa, ya kuma sanya rayuwarmu kamar yadda yake so, tabbas wannan Magana ta mai martaba ta girmama, amma ga amsoshin da zan iya bayarwa a takaice:
1. Farko dai abin da bincikena ya tabbatar min shi ne: daga cikin manyan dalilan da suka sanya shemomin N igeria su ka yi nisa da wajan jifa shi ne saboda kasancewarsu sun fi sauki, sannan ba Nigeria ce kawai take da shemomi ba a Muzdalifa ba, daga cikin kasashen da suke zaune a Muzdalifa akwai: FARANSA, INGILA, MURITANIYA, BANGALADESH, CHAINA, PAKISTAN, INDIA, KARLA, AFGNISTAN, TURKISTAN, da wasu daga cikin Agencies na cikin Saudiyya masu araha.
2. Samawa alhazan Nigeria wuri kusa da wajan Jifa, zai jawo kudin hajji ya kara tsada, ta yadda zai gagari talaka, saboda duk shemar da ta fi kusa da wajan Jifa to tafi tsada.
3. Akwai Agencies da yawa na bakaken fata wadanda suke zaune a kusa da wajan jifa, amma suna da tsada, wannan sai ya nuna ba kasancewarsu ‘yan Afrika ba ne yasa ake ba su wuri mai nisa ba, mas’ala ce ta kudi kawai.
4. Jifan Shaidan ibada ce tabbatacciya daga manzon Allah s.aw, wacce ya yita kuma ya umarci mutane su koya a wajansa, kamar yadda ya tabbata a hadisin da Muslim ya rawaito a lamaba ta: 3197, wannan sai ya nuna hana bakaken fata zuwa jifan Shaidan sabawa nassi ne karara.
5. Dukkan ayyukan da shari’a ta yi umarni da su ba sa rabuwa da wahala, wacce za’a iya jurewa, wannan ya sa aka siffanta su da TAKLIF, kamar yadda ya tabbata a ilimin Usulul-fiqh, Hana Alhazan Nigeria jifan Shaidan saboda wahalarsa, rashin kulawa ne da ka’idojin a ilimin MAKASIDUSHSHARIA.
6. Jifan Shaidan wajibi ne a wajan malamai da yawa, saboda Manzon Allah ya yi shi kuma ya umarci mutane su yi ko yi da shi, In da ace zai kai zuwa ga halaka, tabbas ana iya barinsa saboda ka’aidar: لا واجب مع العجز, duk sanda aka samu kasawa wajan aikata wajibi to yana faduwa, saidai har yanzu ba’a samu ba, tun da Shari’a ta ba da dama yin jifa tun daga safe a ranar sallah har zuwa dare, tun daga zawalin rana a ranakun 11-13, har zuwa dare, yana daga cikin ka’aidojin sharia: Hukuncin sharia yana zagayawa ne da sababinsa.
7. Hukunce-hukuncen sharia ba sa bambanta daga baki zuwa fari, saboda Annabi s.a.w. an aiko shi ne zu wa dukkan mutane kamar yadda aya ta:28 a suratu Assaba’i ta tabbatar da hakan.
8. Ayoyin alqur’aani da hadisan za’a iya jawowa akan faduwar jifa saboda tirmitsitsi, suna Magana ne akan wahalar da ta wuce wacce aka saba da ita,ko kuma wani uziri da sharia ta yadda da shi, amma ba wahalar da aka saba da ita ba a yawancin hukunce-hukunce.
9. Hajji ginshiki ne daga cikin turakun addinin musulunci, wanda yake da bangarori da yawa, barin wani sashe daga cikinsa ba tare da uzuri ba yana iya gurgunta shi, babu mamaki kuma ba za ka sake samun damar yin wani ba.
10. Allah ya sanya ibadoji da yawa a cikin aikin hajji saboda mutane su samu lada cikin sauki, ya kamata ka dage wajan yin kowacce ibada ba tare da nakasu ba, in har ka samu ikon hakan.
Allah ne mafi sani
Dr. Jamlu Yusuf Zarewa
8 Zul-hijja 1437
109/2016