Dalilin koke-koken ‘yan Najeriya game da durkushewar tattalin arzikin kasa, shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis 15 ga Satumba yayi taron gaggawa da ministocinsa da kwararri kan yadda za’a shawo kan al’amarin
Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsaren kasa ta fito da wata sanarwa wadda ke gayama jama’a game da taron inda shugaba Buhari, mataimakinsa Yemi Osinbajo, ministoci da manyan ma’aikatan gwamnati zasu tattauna kan hanyoyin fitarda kasar daga tabarbarewar tattalin arziki.
Buhari tare da Frank Nweke
Hukumar dillancin labarai NAN, tace gwamnatin tarayya ta bayyana wasu daga cikin abinda kasafin kudin 2017 ya kunsa a wajen taron. Ana cewa kasafin kudin na 2017 zai kunshi matakan da zasu bunkasa tattalin arzikin kasar yadda zata fita daga kangin tabarbarewar tattalin arziki. Majalisar zartaswa ta amince da kasafin kudin amma ba’a kaishi ga majalisar kasa ba. Za’a kashe kudade kan manyan ayyukan raya kasa domin farfado da tattalin arzikin kasar. Ga kalaman Buhari a wajen taron:
“Ina mai farin cikin kasancewa tare daku wajen wannan taron kan tattalin arziki da kasafin kudi. Sunan da aka ba taron ‘hada guyawu tsakanin ma’aikatu domin karfafa shirye-shirye da kasafin kudi a Najeriya’ yayi dai dai kuma kan lokaci balle in akayi la’akari cewa muna cikin tsara kasafin kudin 2017
” A cikin shekarun da suka wuce an sami sabani tsakanin burin da aka tsara da abubuwan da aka ci nasara da kasafin kudi a cikin kasar da kuma bangarori. Babu wata nasara da ma’aikatan gwamnatin tarayya suka ci wajen hada kawuna domin nasarar kasa. Wannan ya kawo ci baya ga habaka da ci gaban kasa”