Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya aika ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasiku dauke da shawarwari kan yadda zai magance matsalolin kasar nan.
Advertisements
Bafarawa ya bayyana haka ne yayi wata hira da yayi da gidan rediyon muryar Amurka, inda ya bayyana cewa shugaban kasar baya jin magana, kuma baya daukan shawara.
Bafarawa yace “Buhari ya gaza ne sakamakon rashin jin maganar sa, baya daukan shawara duk da halin da al’ummar kasar ta shiga, na aika masa wasiku da dama, ina bukatar ganawa da shi don mu tattauna hanyoyin gano bakin zaren, amma yaki bani wannan damar.”
Bafarawa ya kara da cewa matsalolin dake damun kasar nan a yanzu sun shafi kowane jam’iyya ne, inda yace don haka dole ne shugaban Buhari ya saurari shawarwarin mutane don ceton kasar.
Bafarawa wanda jigo ne a jam’iyar PDP yace: “rain a yayi matukar baci da yadda wasu dake kiran kawunan su shuwagabannin Arewa sukayi shiru da bakunan su a wannan lokaci da talaka ke ji a jikinsa”
Bafarawa wanda jigo ne a jam’iyar PDP yace: “rain a yayi matukar baci da yadda wasu dake kiran kawunan su shuwagabannin Arewa sukayi shiru da bakunan su a wannan lokaci da talaka ke ji a jikinsa”
A shekarar data gabata ne dai EFCC ta zargi Bafarawa da yaronsa Sagir Bafarawa tare da kamfaninsu Dalhatu Investment Limited da laifin karbar kudaden sata da suka kai biliyan 4.633 daga hannun tsohon mai baiwa tsohon shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro shawara Sambo Dasuki. Shima Dasuki ana zarginsa da karkatar da kusan dala bilyan 2.1 kudaden siyan makamai don yakar kungiyar Boko haram.