*FATAWAR RABON GADO (59)*
Tambaya: Assalamu alaikum, Dr Allah ya karawa rayuwa albarka, tambayata itace mace ce ta rasu tabar mujinta da mahaifiyarta da shakikanta su uku abinda tabari an lissafa jimla 800,000 ya rabon zai kasance.
Amsa: Wa alaikum assalam, Za’a bawa mijinta 400,000, sai a bawa mahafiyarta: 133,333.33333333, ragowar sai a bawa ‘yan’uwa shakikai su raba, duk namiji zai dau rabon mata biyu. Allah ne mafi sani.
*Dr Jamilu Yusuf Zarewa*
27/09/16
27/09/16