FATAWAR RABON GADO (62)
Tambaya?
Assalamu alaykum Warahmatullah. Malam dan Allah Mahaifin mu ya rasu ya bar Mahaifinsa da Matansa 2 da ‘ya’ ya. 11(maza da mata) don Allah malam ya rabon gadon su zai kasance? Mungode Allah yaqarama malam lafiya ya azurta ka da mu da iklasi.
Amsa:
Wa alaikum assalam,
Wa alaikum assalam,
Za’a raba abin da ya bari gida: 24, sai a bawa mahaifinsa kashi: 4, matansa kashi: 3, ragowar kashi: 17, sai a bawa ‘ya’yansa su raba, duk namiji ya dau RABON mata biyu.
Allah ne mafi Sani.
04/10/2016
04/10/2016
DR JAMILU ZAREWA