*FATAWAR RABON GADO (63)*
*Tambaya? *
Assalamu alaykum Warahmatullah, malam inada tambaya. Mace ce ta rasu tabar yaran ta biyu mata sai mahaifinta, da shaqiqanta, to Mallam ya rabon gadon zai kasance, nagode.
*Amsa:*
Wa alaikum assalam,
Wa alaikum assalam,
Za’a raba abin da ta bari gida: 6, sai a bawa ‘ya’yanta mata kashi: 4, sai kuma a bawa mahaifinta kashi: 2. Mahaifinta zai ci kashi daya a matsayin rabonsa (Sudus), ragowar kuma zai dauka saboda shi ne Asibi.
Allah ne mafi sani:
*Amsawa*
*Dr Jamilu Zarewa*
7/10/2016