FATAWAR RABON GADO(65)
Tambaya?
Assalamu alaykum Warahmatullahi ta’ala wa barakaatuhu. Malam barka da war haka. Tambaya ta shine bawan Allah ne yarasu yabar mata daya da ‘ya’ya goma sha daya, goma baligai ne Amma daya karamace wadda kuma mahaifiyar ta bata gidan, to sai duka aka yarda cewa za’ayi sadaka da tufafinsa, dasu sauran kayayyaki Amma banda kudi da gidan dayabari, toh anan malam ya matsayin yin haka ganin cewa akwai karama acikin su? Sannan ya rabon gadon zai kasance? Jazakumullahu khair.
Amsa :
Wa alaikum assalam,
Wa alaikum assalam,
Za’a raba abin da ya bari gida: 8, a bawa Matarsa kashi daya, ragowar kashi bakwan sai a bawa ‘ya’yansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Abin da yake daidai shi ne a jira wacce ba ta balaga har ta mallaki hankalinta. Malamai da yawa sun tafi akan cewa: Uwa ba ta da iko a dukiyar ‘ya’yanta, sai uba ne ke da hakan kamar yadda ya zo a Mugni 5/397. wannan sai ya nuna ba za ta iya yafe Hankinsu ba.

Allah ne mafi sani 13/10/2016
DR. JAMILU ZAREWA