Kyakyawar Budurwa Mai Gemu Ta Shiga Kundin Tarihin Duniya
Advertisements
Daga Ahmadu Manaja Bauchi
A wani sabon rahoton hukumar ajiyar abubuwan tarihi a duniya “Guinness World Records” a bana sun bayyanar da wata matashiya mai shekaru 24 a duniya, a matsayin wadda ta lashe kambun shekarar 2017.
Harnaam Kaur, ‘yar asalin kasar Birtaniya, wadda take da yawan gashin fuska kamar namiji, ta bayyanar da labarin ta, a matsayin wani abun da ta sha wahala, domin kuwa idan aka ganta da gemu da gashin baki, sai a dinga tsokalanta.
Haka ya sa ta shiga cikin damuwa, amma daga bisani ta dauki cewar, wannan wata baiwa ce da Allah yayi mata. Tun tana ‘yar shekara goma sha biyu 12, ta fara gemu, a wannan lokacin ne aka duba lafiyar ta, aka gano cewar, jikin ta yana dauke da wani sinadari dake hana fitowar gashi a jikin mata, ita nata yana da karfi, don haka gashi zai dinga fitowa a jikin ta kamar namiji. Tun dai a wannan lokacin ne ta daina yanke gashin fuskar ta, yanzu haka dai gashin nata yakai tsawon zira’I ko a ce inci shida 6.
A yayin wani bukin nuna kawar kaya, Harnaam, ta gabatar da kanta a matsayin mace da tafi yawan gashi a tsakanin mata, hakan ya jawo hankalin mutane da dama a kasar Ingila.
Ta bayyanar da cewar, wannan baiwa ce daga Allah, don haka kada wani ko wata su raina irin baiwar da Allah ya yi musu a rayuwa. Hasalima sai su gode mishi, domin yanzu gashi ta shiga cikin tarihin duniya.