Da Yardar Allah Buhari Zai Zarce A Zaben 2019, Idan Ya Gama Kuma Ni Zan Maye Gurbinsa A Zaben 2023, Inji Hanarabul Gudaji Kazaure
Dan Majalisa mai wakiltar Kazaure, Roni, ‘Yan Kwashi a Majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Jigawa, Honorobul Muhammadu Gudaji Kazaure a wani hira da aka yi da shi ya bayyana cewar idan Allah ya kai mu a shekarar 2019 Buhari zai zarce da yardar Allah ko da abokan gaba ba sa so. Sannan ya kara da cewar bayan Buhari ya gama shekarunsa 8 a shekarar 2023 shi zai mikawa mulkin Nijeriya, wannan shine fatanshi.
Dan Majalisar, dukda yadda ya shahara da ba da dariya a dakin majalisar wakilai ta tarayya, a hirar da aka yi da shi ya nuna da gaske yake yi, domin a cewarsa, Nijeriya na bukatar shugaban kasa matashi, shugaban majalisar dattijai da na wakilai duka matasa, bayan Buhari ya gama nashi mulkin.
Masu karatu me za ku ce kan hakan?