DUKIYAR KASA TA GWAMNATI CE ! ! !
Tambaya?
Assalamu alaykum, malam da fatan kana lafiya,
Tambayata itace :-
Shin wa yake da ikon tasarifi cikin dukiyar kasa, gwabnati kadai ko talakawa ma suna da rabo a ciki ?.
Saboda Na ji wani Malami a Radio yana cewa dukiyar kasa ta gwabnati ce, talaka baya da rabo a cikin ta.

Kubamu fatawa Allah shi saka muku da Alkairi.
Amsa :
Wa alaikum assalam, Shugaba shi ne yake da ikon tasarrufi a dukiyar kasa, saidai ya wajaba amfanin da zai yi da dukiyar ya zama gwargwadon maslahar talakawan da yake mulka saboda fadin Annabi S.a.w. (Dukkanku masu kiwo ne, kuma za’a tambaye ku akan abin da kuke kiwo) kamar yadda Muslim ya rawaito. Tabbas Allah zai tambayi Shugaba idan ya barnatar da dukiyar al’uma ba bisa ka’ida ba.
Bukhari ya rawaito hadisi, Annabi S.A.W. yana cewa: (Tabbas za ku yi kwadayin shugabanci amma kuma zai zama nadama, madalla da darbar da za’a samu a lokacin shugabanci, saidai abin da zai biyo baya a lahira ya munana), wannan yana wajabtawa Shugaba taka-tsantsan da kuma tuna lahira idan yana kan kujerarsa.

Allah ne mafi sani:
27/10/2016
DR. JAMILU ZAREWA