TARON SUNA GA MATA HALAL NE ! ! !
Tambaya?
Assalamu Alaikum, Malam don Allah menene hukuncin taron bikin suna a Musulunci ?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
A zahiri taron sunan da mata suke yi al’ada ne, tun da mata ba sa yinsa da nufin samun lada ko karawa abin da aka haifa albarka. Mata suna yinsa ne don taya juna farin ciki, da kuma nuna annashuwa saboda karuwar da aka samu, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al’adu da mu’amalolin mutane a bude yake, sai abin da sharia ta haramta.

Duk Wadda take taron suna ba tare da ta riya cewa ibada ba ce hana ta ko bidi’antar da taron yana da wuya, tun da ba mu da dalilin SHARIA da ya haramta.
Idan a cikin taron aka samu bidi’o’i ko kuma ayyukan da Allah ya haramta kamar fito da tsaraici, ko zancen da Allah ya hana, hakan zai iya zamar da shi haramun, saboda yana daga cikin sharudan lura da al’ada kar ta zama da sabawa nassoshin SHARIA, ko kuma ka’idojin da malaman musulunci suka cimma daidaito akan su, kamar yadda malaman Usul da na Kawa’idul Fiqhiyya suka ambata.
Allah ne mafi sani
7/11/2016
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa