*FATAWAR RABON GADO (75)*
*Tambaya*
Assalamu alaikum. Allah ya karawa DR lafiya.tambaya : mutum ne ya rasu ba shi da uwa da uba, saidai ya bar yayyensa da mata da maza da yaro namiji da kuma matarsa yaya rabon zai zama ?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida takwas, a bawa matarsa kashi daya, Ragowar kashi bakwan sai a bawa dansa saboda shi asibi bi ne. ‘Yan’uwa ba sa gado mutukar mamaci yana da *DA* namiji.
Allah ne mafi sani.
10/11/2016
10/11/2016
*Amsawa*
*DR Jamilu Zarewa*