• Ya wajaba Dalibi ya rinka yin hadda a wajan malami saboda ya dinga gyara masa.
• Ka da Dalibi ya dinga haddace abu mai yawa, musamman farkon fara haddarsa, saboda wannan zai jawo ya yi hadda mara karfi, ya kamata ya dinga yi daidai yadda zai iya yin muraja’a sosai, don ya inganta haddarsa.
• Idan dalibi zai fara hadda ya fara daga suratu Annas saboda ta fi sauki.
•Ya rinka yin hadda da al- qur’ani iri daya, saboda zai sa shi ya dinga tuna gurin da kowacce aya ta ke, da kuma tuna inda kowanne shafi ya ke karewa.
• Ya wajaba ya ware wani lokaci na musamman domin muraja’ar abin da ya haddace.
Dauba khuduwatun ilassa’adah
Amsawa
Dr.jamilu zarewa