SHIN AZUMIN ASHURA YANA KANKARE MANYAN ZUNUBAI ?
Tambaya :
Malam ina da tambaya, Irin ayyuka na azumin ashura arfa, Misali na ashura kaffarane na shekarar da ta gabata, Shin malam yana kankare manyan zunubai irin su shirka, mua’mala da kudin ruwa da sauransu, Malam yaya maganar magabata game da tambayata.

Amsa :
To dan’uwa hadisi ya tabbata daga Annabi s.a.w cewa : Azumin ashura yana kankakare zunubin shekara daya” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1162.
To dan’uwa hadisi ya tabbata daga Annabi s.a.w cewa : Azumin ashura yana kankakare zunubin shekara daya” kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1162.
Malamai magabata suna cewa azumin ashura da na Arfa suna kankare kananan zunubai ne kawai, amma manya sai an tuba Allah yake gafarta su, sun kafa hujja da fadin Annabi s.a.w, inda yake cewa :
“Salloli guda biyar da Ramadhana zuwa Ramadhana suna kankare abin da yake tsakaninsu, mutukar an bar manyan zunubai” Muslim a hadisi mai lamba ta : 233 .
Wannan hadisin yana nuna cewa : sallolin farilla da azumin Ramadhana ba sa kankare manyan zunubai, ka ga kuwa ta yaya azumin nafila kamar na ashura da na ranar Arfa zai kankare su ?
Wannan ita ce maganar Nawawy a littafinsa Alminhaj sharhin sahihi Muslim a 4/308, da kuma Ibnul-kayyim a littafinsa : Aljawabul-kafy shafi na : 13 .
Allah ne mafi sani .
Amsawa
Dr jamilu zarewa