SHIN SAYYIDINA UMAR YA TABA BINNE ‘YARSHI ?
Tambaya :
Assalamu alaikum malam, shin don Allah ina gaskiyar lamarin da ake cewa : Umar yana kuka wataran kuma sai a ga yana dariya, har aka tambaye shi, sai yake cewa : ya tuna ‘yarsa da ya rufe a zamanin jahiliyya shi ne yake kuka ?

Amsa :
To dan’uwa tabbas wannan maganar ta yadu a wajan masu wa’azi da masu huduba akan minbarai, saidai ba ta da tushe, kuma karya ce, saboda abubuwa kamar haka :
To dan’uwa tabbas wannan maganar ta yadu a wajan masu wa’azi da masu huduba akan minbarai, saidai ba ta da tushe, kuma karya ce, saboda abubuwa kamar haka :
1. Masana tarihi sun tabbatar da cewa : matar Umar R.A ta farko a rayuwarsa, ita ce Zainab ‘yar Maz’un wacce ta Haifa masa Hafsan da Annabi s.a.w. ya aura, don haka Hafsa ita ce babbar ‘yarsa, kuma da ita ake masa alkunya, don haka idan bai rufe babba ba daga cikin ‘ya’yansa, ta yaya zai bunne wacce ta zo daga baya ?, tare da cewa :
ita kan ta Hafsan an haife ta ne kafin a aiko Annabi s.aw. da shekara biyar, ka ga kenan abin da ta riska na jahiiliyya ba shi da yawa .
2. Wacce ake cewa Umar ya bunneta da ranta, gaba daya littatafan tarihi ba su fadi labarinta ba, ko su kirga ta a cikin ‘ya’yansa ba.
3. Sannan kabilar Adiy wacce Umar ya fito daga cikinta ba su shahara da binne ‘ya’ya mata ba, a zamanin jahiliyya.
4. Dogon bincike ya nuna cewa : babu wannan kissa kwata-kwata a cikin littattafan Ahlussunah, asalinta daga littatafan ‘yan shi’a aka cirota, don haka su ne suka kirkire ta, dama kuma sun saba yin kage ga sahabban Annabi s.aw.
Allah ne mafi sani .
Don neman Karin bayani duba : Dirasa nakdiyya fi shaksiyati Umar 1/111. ﺩﺭﺍﺳﺔ ﻧﻘﺪﻳﺔ ﻓﻲ ﺷﺨﺼﻴﻴﺔ ﻋﻤﺮ ﺑﻦ ﺍﻟﺨﻄﺎﺏ ﻭﺳﻴﺎﺳﺘﻪ ﺍﻹﺩﺍﺭﻳﺔ 1/111 –
Amsawa
Dr jamilu zarewa