Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh, malam ina da tambaya, mutum ne ya mutu ya bar matan aure biyu da yayye biyar *shakeekai* namiji daya, sauran hudun matane, yaya rabon gadon su zai kasance
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari kashi:4, matansa biyu su dau kashi daya, Ragowar kashi ukun sai a bawa yayyensa tun da duk dakinsu daya, duk namiji ya dau rabbon Mata biyu.