Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home ยป SHIN ANNABI MUHD S.A.W. NE FARKON HALITTA ? | DR JAMILU YUSUF ZAREWA
FATAWA

SHIN ANNABI MUHD S.A.W. NE FARKON HALITTA ? | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

iGeekBy iGeekDecember 3, 2016No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

SHIN ANNABI MUHD S.A.W. NE FARKON HALITTA ?

Tambaya :
Malam ina da wata tambaya wacce ta daure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka bani tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Allah Annabi Muhammad ne ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shine sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?

Advertisements


AMSA :
Wa alaikum assalam
Akwai hadishin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi s.aw. shi ne farkon wanda aka fara halitta, saidai hadishin bai inganta ba, 
wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin karya ne.

Fadin cewa Annabi s.a.w. shi ne farkon wanda aka halitta ya sabawa alqur’ani, ta bangarori da dama ga wasu daga ciki :

1. Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba daya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi MUHD shi ne farkon halitta hakan ya sabawa ayoyin alqur’ani.

2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad s.a.w., tun daga mahafinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.

Zance mafi inganci shi ne : farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al’arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa : “Allah ya kaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al’arshinsa yana kan ruwa”

Kin ga wannan yana nuna cewa Al’arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi muhd s.a.w.
Allah ne mafi sani.
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Yawun Bakin Budurwa Yana Kara Karfin Hadda Al-kur'ani inji Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

March 12, 2018

Khudubar Ranar Juma'a Mai taken Sulhu Alheri ne Dr Muhammad Sani Umar R/lemo

February 18, 2018

[Audio] Download Raddi Mai Taken 'Babban Bola' ? Sheikh Bello Yabo Sokoto

July 24, 2017
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.