HUKUNCIN SADUWA DA MAI HAILA ! !
Tambaya?
Assalamu Alaikum! Mallam ina tambaya idan mutum ya sadu da matarsa tana haila me ya kamata yayi?, kuma ina neman cikekken bayani mallam.
Amsa :
Wa alaikum assalam,
Wanda ya sadu da matarsa tana haila, ya wajaba ya yi istigfari saboda ya aikata abin da Allah ya hana a aya ta: 222 a suratul Bakara, Wannan ita ce maganar mafi yawan malamai kamar yadda Ibnu Rushd ya fada a Bidayatul mujtahid.
Hadisin da ya zo na cewa: (Wanda ya sadu da matarsa tana haila ya yi sadaka da rabin dinare) bai inganta ba, wannan yasa ba za’a iya gina hukunci akansa ba.
Allah ne mafi sani
27/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA