- SHEIKH (Dr.) BASHIR ALIYU UMAR: KWARARREN MALAMIN SUNNAH!!!
Yana daga cikin baiwar da ALLAH yake yiwa bayinsa kebantattu, shi ne ya hore musu bai ta ilimi. Hakika, Allah ya yiwa Dr. Bashir Aliyyu Umar baiwa ta ilimi a fannoni da dama, bayan kasancewarsa Injiniya ne, kuma kwararren Malamin kimiyyar Hadisi ne. Malam ya karanta Ilimin Hadisi da kimiyyarsa a Jami’ar Musulunci ta Islamic University of Madinah tun daga matakin Degree na farko har zuwa Degree na uku inda Malam ya yi Kimiyyar Hadisi wato (PhD, Hadith Sciences).Allah ya yiwa Malam Bashir hikima da kaifin kwakwalwa, da sanin hukunce-hukuncen da suka shafi Ilimin Fiqhu, Allah ya bashi hazaka, da iya warware mas’aloli cikin hikima da ilimi.
Bayan kasancewar Dr. Bashir kwararren Malamin Sunnah, Malam Marubuci ne na Hausa da Turanci, domin ya rubuta litattafai da dama wasu anbuga su tuntuni wasu kuma ba’a kai ga buga su ba. Malam ya rubuta litattafai da daman gaske kamar The Methodology of Imam Ahmad regarding the inconspicuous weaknesses of hadith narrations, Garkuwar Musulmi ta Addu’o’i daga Alkur’ani da Sunnah; Hausa translation of Hisnul Muslim Min Adhkaaril Kitaab was Sunnah, Na Dr. Sa’eed bin Wahf Al Qahtani, Useful Ways of Leading A Happy Life, Fadakarwa Kan Hukunce-Hukunce da suka kebanci Mata Muminai. Wadannan su ne kadan daga cikin irin dumbin litattafan da Malam Bashir ya rubuta a cikin Ingilishi da Hausa, bayan haka kuma, akwai wasu litattafai da Malam ya rubuta wadan da ba’a kai ga buga su ba kamar: Between the Companions and Members of the Household of the Prophet, may Allah bless him and grant him peace, 55 rules regarding the inconspicouos weaknesses of hadith narrations and their applications among the scholars of hadith (an original work), Takhreej Nusoos ‘aml ahlil Madinah fil Muwatta wal Mudawwanah da sauransu da dama.
Malam Bashir kwararre ne wajen sanin Ilimin Aqeedah, ya yi fice sosai a wannan fage, haka kuma masani ne a sauran fannoni Ilimai da dama, kuma masanin siyasar duniya, kuma Masanin Tattalin Arziki Bisa koyarwar Shar’ah, uwa uba kuma Malam Bashir Mahaddacin AlQur’ani ne, Ya Salam! Malam Bashir Mutum ne mai kan-kan da kai ga tawalu’u, yana girmama ilimi yana kuma girmama malamai masu Ilimi. Watarana, wasu al’amura guda biyu sun faru akan idona, Na farko wani ya zowa da Malam Bashir da wata fatawa, amma sai ya tambayi meye ra’ayin abokinsa Dr. Muhd Umar akan wannan fatawa. Abu na biyu kuma, wani ya tambayi ra’ayinsa dangane da kalaman da Barack Obama ya yi a lokacin da ya kai ziyara kasar Masar ga Musulmin duniya, a lokacin Dr. yace mu saurara muji ra’ayinsu Sheikh Dr. Yusuf Qardawi tukuna. Wannan ya kara nunamin irin yadda Malam Bashir yake taka-tsantsan da Ilimi da kuma girmama maganganun Manyan Malamai.
Malam Bashir mutum ne wanda duk mutumin da Mu’amala ta hadasu da shi, sai ya fadi alkhairinsa da kirkinsa, da kaunarsa da jama’a. Mutum ne salihi, Allah ya bashi baiwar iya rike sunayan mutane, Yau zaku yi Mu’amala da Malam, Insha Allah bayan shekara guda idan ka dawo zai ambaci sunanka, bai cika manta suna mutanan da ya yi mu’amala da su ba. Allah ya bashi wannan baiwar.
Sannan kuma, Malam Bashir kusan yana daga cikin mutanen sahun gaba wadan da suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin tabbatar Bankin Musulunci a Najeriya. Da shawarwarinsu da maganganunsu da hangen nesansu wannan alkhairi ya tabbata da dumbin al’ummah ke cin mariya a yanzu. Hakika Malam Bashir yana daga cikin kalilan din mutane da Allah ya yiwa tarin baiwa mai yawa da dumbin hikimomi. Na tabbata idan da za’a tara mutum goma da suka san Malam Bashir zasu yi rubuce-rubuce mabambanta wajen bayanin waye Malam Bashir. Tabbas Dr. Bashir Aliyu Umar kwararren Malamin Sunnah ne a wannan zaminin a Najeriya ta Arewa. Sautinsa bai tsaya iyakar Arewacin Najeriya ba, wajen kira zuwa ga Allah da Tauhidi, sautinsa ya karade kasarnan da sauran kasashen Afurka da Asiya da Gabas ta Tsakiya. Allah ya sakawa Malam Bashir da alheri, ya sanya albarka a cikin rayuwarsa da iliminsa da zurriyarsa. Allah ya yawaita mana irinsu.