SANYA BAKAKEN TUFAFI DA DUKAN JIKI A RANAR ASHURA DA SUNAN BAKIN CIKI DA RANAR DA AKA KASHE HUSAINI (RA).
Babu shakka ranar Ashura rana ce wacce Allah subhanahu wata’ala ya girmama jikan Manzon Allah (saw) da samun shahada, wacce ta qara nuna girmansa da darajarsa a wajen Allah.
Sayyadina Husain mutum ne mai daraja, manzon Allah (saw) yana kaunarsa shi da yayansa Alhassan, kuma yana kusanto su zuwa gare shi, har ma ya fada game da su cewa su ne shugabannin samarin Aljanna.
Allah subhanahu wata’ala ya kaddara ma sa shahada bayan da mutanen KUFA (babbar cibiyar shi’anci a wancan lokacin) su ka yaudare shi suka ce ya zo za su yi ma sa mubaya’a a matsayin khalifa shi kuma ya gaskatasu ya amsa gayyatarsu. A gefe guda kuma manyan masoyansa Abdullahi bin Umar da Abdullahi bin Abbas su na ta kokarin hana shi tafiya tunda sun fahimci yaudarar da ke cikin gayyatar.
Advertisements
Al Imam ibn Kasir ya hakaito cewa bayan Abdullahi bin Abbas (ra) ya bawa sayyadina Hussain (ra) shawarar kar ya amsa gayyatar shi kuma ya dage kan sai ya tafi, sai Ibn Abbas (ra) ya sake dawowa bayan kwana biyu wajen Sayyadina Husain (ra) ya ce da shi: “Ya dan baffa na, na yi qoqarin na haqurqurta da raina kan tafiyarka amma na kasa haquri, ina matuqar ji ma ka tsoron wannan tafiyar, domin mutanen Iraq mayaudara ne, don haka kada ka rudu da su, ka yi zamanka a nan Makkah har mutanen Iraq su gama da abokan adawarsu sannan sai ka je mu su, idan kuma ka dage sai ka tafi, to ka tafi yaman domin a can akwai jama’ar da za su baka kariya, kuma mahaifinka ya na da magoya baya a can, kuma idan ka je can din ma ka yi nesa da su, ka fara aika mu su da wasiqar manufar zuwanka, idan ka yi haka ina sa ran za ka sami abin da ka ke so.”
Abdullahi ibn Zubair (ra) y ace da Sayyadina Husain (ra): “Yanzu za ka tafi wurin mutanen da su ka kashe babanka su ka soke dan uwanka?” sai sayyadina Husain yace: “gara a kashe ni a guri kaza da azo ma ka a hantata.”
Shi ma Abdullahi ibn Umar (ra) da ya ji labarin Sayyadina Husain (ra) zai tafi sai ya garzayo ya same shi bayan ya yi tafiyar kwana biyu ko uku, ya ce da shi: “Ina zaka?” sai sayyadina Husain (ra) yace: “Iraq” sai ya fito da tulin takardu ya nuna Ibn Umar (ra) y ace: “wadannan wasiqun su ne da su ka aiko min su na yi mini mubaya’a.” sai Ibn Umar (ra) ya ce da shi ka da ka je. Sai ya qi, sai Ibn Umar (ra) yace bari na gaya ma ka wata magana: “haqiqa Mala’ika Jibril (A.S) ya zo wajen manzon Allah (saw) ya kuma ba shi zabi tsakanin duniya da lahira sai ya zabi lahira bai zabi duniya ba, kai kuma tsoka ce da jikin manzon Allah (saw) don haka babu wanda zai jibinceta a cikinku, kuma Allah bai kawar da ita daga gare ku ba sai don ya zaba muku abinda ya fi ta alheri.” Duk da haka Sayyadina Husain (ra) ya dage sai ya tafi, sai Abdullahi ibn Umar (ra) ya rungume shi ya na kuka ya na yi ma sa ban kwana. – Ibn Kasir, al-Bidaya wannihaya, (11/496-498), madaba’ar Hajar-Aljiza. Shekarar bugawa 199.
Allahu akbar! KADDARA TA RIGA FATA! Sayyadina Husain (ra) ya tafi Iraq, su kuma mutanen kufa su ka tsare shi a wurin da ake kira KARBALA, su ka hallaka shi. Allah Ya qara Rahama a gare shi.
Dama Allah ya kan jarrabi bayinsa ne gwargwadon karfin imaninsu, kamar yadda ya tabbata daga Mus’ab bn Sa’ad (RA) yace na tambayi manzon Allah (saw) na ce: “Ya ma’aikin Allah! su waye su ka fi shiga cikin tsananin bala’i? sai yace: “Annabawa, sannan wadanda su ke jin tsoron Allah mataki bayan mataki. Ana jarrabar mutum gwargwadon addininsa, idan addininsa mai karfi ne sai bala’insa ya tsananta. Idan kuma addininsa mai rauni ne sai a jarrabe shi gwargwadon addininsa. Bala’i ba zai gushe ga bawa ba, har sai ya kasance yana tafiya a kan kasa ba shi da wani zunubi a kansa.” (Tirmidhi: 2398. Kuma yace Hadisi ne Hasanun Sahih)
Su kuma Alhasan da Husain (RA) su na daga cikin wadanda Allah ya kaddara mu su matsayi madaukaki, kuma an haife su a lokacin da musulunci ya tsaya da kafafunsa, kuma sun taso a cikin buwaya da karamci, dukkanin sahabbai su na girmama su, kuma manzon Allah (saw) ya koma ga Allah tun su na kanana. Domin Allah ya cika mu su ni’imarsa a gare su sai ya jarrabe su a karshen rayuwarsu, ta yadda aka yi mu su kisan gilla Allah ya azurta su da shahada.
Don haka duk musulmi na gari yana jin ciwon kisan gillar da aka yi wa Sayyadina husaini RA) kamar yadda yake jin ciwon kisan gillar da aka yi wa Sayyadina Aliyyu da sayyadina Umar da Sayyadina Uthman Allah ya kara yarda a gare su.
Sai dai mumini idan musiba ta same shi maida lamarinsa yake yi ga Allah. kamar yadda Allah yace:
“…. Ka yi wa ma su hakuri bushara, su ne wadanda idan musiba ta same su, suke cewa lallai mu daga Allah muke, kuma lallai mu ma su komawa ne gareshi. wadananan suna da daraja da rahma daga ubangijinsu kuma wadannan su ne shiryayyu”. (Baqara 155-156).
Sannan kuma hadisi ya tabbata daga Annabi (saw) yace: “Babu wani musulmi da za’a jarrabeshi da wata musiba yace Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, ya Allah ka bani lada a cikin wannan musiba da ta same ni ka musanya mini da mafi alkhairinta. Face Allah ya musanya ma sa da mafi Alkhairinta.” (Muslim:1525)
Wannan shi ne abinda ya kamata kowa ne mumini ya yi yayin da kowace irin musiba ta same shi amma maimakon haka sai shaidan ya jefa mutane cikin bidi’oi ta sababin wannan mutuwar.
Bidi’a ta farko ita ce: Bakin ciki da kuka da marin fuska da hargowa da jiyar da kai kishirwa.
Bid’ah ta biyu kuma ita ce: sanya bakaken kaya da jima kai rauni da wakokin nuna jimami wadanda sukan kai ga zagin manyan sahabbai wadanda su ke da rigaye da falala a cikin wannan addinin da la’antarsu da shigar da wanda ba shi da laifi cikin laifi, da karanta labaran yadda aka kashe shi wandanda su ke cike da tatsuniyoyi da karerayi.
Babbar manufar wadanda su ka shirya wadannan abubuwan ita ce bayarda kofar fitina da rarraba kan al’umma. Domin dukkan musulmi sun yi ijima’i kan abinda su ke yi ba wajibi ba ne ko mustahabbi. Bari ma dai raki da kukan kera saboda musibar da ta riga ta faru, yana daga mafin girman abinda Allah da manzonsa suka haramta.
Kuma da hakan yana da wani asali to da mahaifinsa sayyidina Aliyu (RA) ya kamata a fara yiwa wannan tunda shi ma kashe shi aka yi, kamar yadda kowa ya sani. Kuma mutuwar manzon Allah (saw) ita ce mafi girman masifa ga al’ummarsa, amma ba mu taba jin cewa wani daga cikin sahabbai ko ahlil baiti sun yi taro a kowace shekara don nuna jimami da baqin cikin wannan babban rashi ba, wanda da hakan alheri ne da sun rigaye mu. Tunda ba su yi ma sa ba kuwa, to lalle yi wa wanda bai kai matsayinsa ba bidi’a ce mummuna abar kyama, musamman ma idan muka yi duba da cewa manzon Allah (saw) ya hane mu yin koke-koke da marin fuska yayin musiba kuma yace yin haka aiki ne na mutanen jahiliyya wadanda basu san addini ba. Manzon Allah (saw) yace:
“Baya cikinmu wanda ya mari kuncinsa ko ya yaga wuyan rigarsa ko ya yi da’awa da da’awa irin ta jahiliyya.” (Bukhari: 1294)
Haka nan hadisi ya tabbata daga Abdullahi bn Mas’ud (RA) yace: “hakika ni babu ruwana da wanda manzon Allah (saw) ya nuna babu ruwansa da shi.
“Lalle manzon Allah (saw) babu ruwan sa da mai kururuwa yayin musiba, da mai aske kansa yayin musiba, da mai keta tufafinsa ko jikinsa yayin musiba.” (Mulim:104)
Saboda wadannan dalilai ne muke kira ga al’ummar musulmi da su guji irin wadannan tarurrukan da su ka sabawa littafin Allah da karantarwar manzon Allah (saw) da fahimtar magabata na kwarai wadanda babu abinda yake cikinsu sai rudani da yaudarar ma su qarancin ilmi wadanda ba su fahimci addininsu ba.
Don haka ya kamata wadanda suke riqar ashura ranar biki ko idi su sani da yahudawa suke koyi ba da manzon Allah (saw) ba. Domin manzon Allah (saw) AZUMI ya yi, kuma ya kwadaitar da al’ummarsa falalar yinsa, kamar yadda ya zo a cikin sahihi Muslim cewa: an tambayi Manzon Allah (saw) game da azumin ashura sai yace: “Yana kankare zunuban shekarar da ta gabata.” (Muslim: 1162)
Amma sanya baqaqen tufafi a wannan ranar ko kuma watanta daga cikin ranaku da sunan ibada; wannan ba shi da asali a cikin addinin musulunci. Bari ma dai litattafan shi’a Rafida sun kushe sanya baqaqen tufafi a matsayin wata alama ta addini.
Ga misalign kadan daga maganganun malamansu akan hakan:
1. Assaduk ya rawaito da isnadinsa zuwa Ja’afar Assadiq (A.S) yace: “Allah ya yi wahayi ga wani annabi daga annabawansa, (yace da shi) kace da muminai kada ku sanya tufafin maqiyana, kada ku ci abincin makiyana, kada ku bi tafarkin maqiyana sai ku zama maqiyana kamar yadda su ke maqiyana.” (Duba Alfaqih(1/252), da Wasa’ilish shi’ah (4/384), da Biharul Anwar (2/291).
Don sanin wadanne irin tufafi ne tufafin makiyan Allah da su ke cewa kada a sanya duba littafinsu mai suna “Uyunul Akhbar” daga Sayyadina Aliyu daga manzon Allah (saw) yace: “Lallai tufafin makiya na su ne bakake.” (Duba Uyunul Akhbar 1/26).
2. Haka nan an rawaito daga Abi Abdillah (A.S) wani mutum ya tambaye shi ko zan iya yin sallah da baqar hula? Sai yace:
“Kada ka yi sallah da ita domin ita tufafin ‘yan wuta ne.” (Duba Alwasa’il (3/281) Babi na 20, Hadisi na 3 cikin Babu Libasil Musalli. Da Alfaqih, na Assaduq (2/232).
3. Alhurrul amili ya rawaito daga saduq daga Sayyadina Aliyyu (RA) yace da sahabbansa: “Kada ku sanya bakaken tufafi domin haqiqa su tufafin FIR’AUNA ne.” (Duba Man La Yahduruhul Faqih, (1/251), da Alwasa’il, (3/278) cikin Abwabul Libas.)
Wadannan ‘yan dalilai da su ka fito daga litattafan jagororin ma su sanya bakaken kaya a matsayin wata alama ta addini sun isa su sa ma su yi su gane batancin abinda suke yi. Allah ka bamu ganewa amin.
– Daga littafin ZARARREN TAKOBI AKAN BIDI’O’IN WATANNIN SHEKARA Na Sheikh AbdulWahhab Abdallah.