FATAWAR RABON GADO (86)
Tambaya?
Assalamu alaykum.
Tambayata shine idan mamaci ya rasu ya bar yara mata guda4 da mata 1 sai mahaifiyarsa bai da yaro namiji ko daya shin dan uwansa wato yayansa xa.a iya rava gadon da shi?
Tambayata shine idan mamaci ya rasu ya bar yara mata guda4 da mata 1 sai mahaifiyarsa bai da yaro namiji ko daya shin dan uwansa wato yayansa xa.a iya rava gadon da shi?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
Wa alaikum assalam,
za’a raba abin da ya bari gida: 24, sai a bawa matarsa kashi: 3, ‘ya’yansa Mata kashi: 16, mahafiyarsa kashi: 4. Idan dan’uwansa da ka ambata shakiki ne ko li’abbi sai ya dauke kashi dayan, in uwa daya kawai aka hada da shi ba zai yi gado ba, tun da mamacin yana da ‘ya.
Allah ne mafi sani
18/11/2016
DR. JAMILU ZAREWA