HUKUNCIN AMARYAR DA TAYI ZINA
TAMBAYA TA 2081
********************
Assalamu Alaikun Da Fatan Mallam Yana Lafiya Tare Da Iyalansa Baki ‘Daya, Mallam Tambayata Itace Meye Hukunci Amaryar Da Tayi Zina Saura Kwana Bai wuce hudu 4 Auren ta, Kuma Yaya Auren Yake A Musulunci, Saurayin da sukayi Zinan Bema san Aure zatayi Ba, kuma bata sanar cewa aure ba, Me Hukunci Shi Saurayin.
********************
Assalamu Alaikun Da Fatan Mallam Yana Lafiya Tare Da Iyalansa Baki ‘Daya, Mallam Tambayata Itace Meye Hukunci Amaryar Da Tayi Zina Saura Kwana Bai wuce hudu 4 Auren ta, Kuma Yaya Auren Yake A Musulunci, Saurayin da sukayi Zinan Bema san Aure zatayi Ba, kuma bata sanar cewa aure ba, Me Hukunci Shi Saurayin.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wannan auren nata bai yiwu ba. Dole a warwareshi taje tayi Istibra’i sannan a sake daurashi.
Akwai fuskoki biyu da suka nuna rashin halaccin auren :
FUSKA TA FARKO: A karkashin addinin Musulunci bai halatta a daura ma mace aure da wani sabon Miji ba, har sai ta tabbatar da cewar babu komai acikkn mahaifarta. Bisa wannan dalilin shi yasa Mata suke yin iddah bayan sun fita daga hannun Mijinsu kafin su sake aurar wani Mijin.
Hakanan duk Matar da tayi Zina, ko budurwa ce ko bazawara bai halatta adaura Mata aure har sai tayi Istibra’i. Wato Jini uku, ko kuma a Qalla jini guda (a fa’dar wasu Maluman).
To idan har Mace tayi aure ba tare da yin Istibra’in nan ba, Malamai sun ce auren bai yiwu ba. Ba za’a kira irin wannan zaman da sunan “AURE” ba. Har sai an warwareshi taje tayi Istibra’i sannan a sake daura sabon aure da sabon sadaki.
FUSKA TA BIYU : Duk Matar da ta zamanto ita Mazinaciya ce, to bai halatta a daura mata aure da cikakken Mumini wanda ba ya Zina ba.
Hakanan duk Namijin da ya zamanto shi Mazinaci ne, bai halatta ya auri Matar da bata yin Zina ba.
Sai dai idan sun tuba, Ita Mazinaciyar tayi istibra’i. Sannan zai halatta Mumini ya aureta.
Allah ne ya fada acikin ayah ta Uku acikin Suratun Nuur.
Al Imam Ahmad bn Hanbal ya ruwaito hadisi daga Sayyiduna Abdullahi bn Amru bn Al-Aas (ra) yace :
“Wani Mutum Mumini ya nemi izinin Manzon Allah (saww) akan yana so zai auri wata Mata mai suna UMMU MAHZOUL wacce ta kasance kowa ya san tana yin Zina.
Sai Manzon Allah (saww) ya karanto masa wannan ayar ta cikin Suratun Nuur :
“MAZINACI BA ZAI AURA BA SAI DAI MAZINACIYA KO MUSHRIKA. KUMA MAZINACIYA BABU MAI AURENTA SAI MAZINACI KO MUSHRIKI. KUMA AN HARAMTA WANNAN BISA MUMINAI”.
(Aduba Hadisi na 11359 acikin Sunanul Kubrah ta Imamun Nisa’iy).
Hakanan akwai wani Sahabi mai Suna MARTHAD IBNU ABI MARTHAD (ra) ya ta’ba neman izini awajen Annabi (saww) cewa yana so zai auri wata Mata mai suna ‘UNAAQ” ta kasance Mazinaciya ce agarin Makkah.
Sai Manzon Allah (saww) yayi shuru bai bashi amsa ba, har sai da wannan ayar ta cikin Suratun Nuur ta sauka.
Aduba Sunanu Abi Dawud hadisi na 2051. Da kuma Sunanun Nisa’iy juzu’i na 6 shafi na 66 acikin kitabun Nikahi.
Duk da cewa akwai Malumab da suke ganin cewa wannan ayar Mansukhiyah ce, to amma Bisa wadannan hujjojin ne Malamai irin su Imamu Ahmad suka dogara. Sun ce bai halatta a auri duk Matar da tayi zina ba, har sai bayan ta tuba.
To kaga ita wannan baka ambaci tubanta ba, kuma kace tayi aure da wani bayan kwana hudu. Don Haka auren nata bai dauru ba.
Matsayin shi Saurayin shine sunansa Mazinaci Kuma lallai laifin zinar yana nan akansa. Idan bai tuba ba, yadda yayi haka shima za’ayi masa. Kafin kuma ya koma ga Allah ya karbi sakamakon abinda ya aikata.
WALLAHU A’ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (05-01-2017).