HUKUNCIN MAI AZUMIN DA BA YA SALLAH
TAMBAYA TA 2080
*******************
Assalamun alaikum, fatan mallam ansha ruwa lafya. Mallam dalibikane daga zauren fiqhu facebook. Ina daukeda tambayoyi 3 dan Allah mallam ataimaka a amsa min.
*******************
Assalamun alaikum, fatan mallam ansha ruwa lafya. Mallam dalibikane daga zauren fiqhu facebook. Ina daukeda tambayoyi 3 dan Allah mallam ataimaka a amsa min.
1-miye hukunci mai azumi da baya sallah, ya azumin sa yake?
2- Magajiyata ke fama da ciwon awazu, hakan ya janyo ta sha azumi 2, dan Allah mallam ataimaka.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Sallah da azumi dukkansu suna daga cikin rukunan Musulunci din nan guda biyar. Kuma duk wanda ya bar wani daga cikinsu, lallai ba za’a kirashi cikakken Musulmi ba.
Idan mai Azumi ya zamanto ba ya yin sallah, to wannan bai karya masa azuminsa ba. Sai dai kuma Allah ba zai karbi azumin nasa ba. Wato babu lada kenan.
Idan kuma lalaci ne yasa ba ya yinta, to sai ayi masa wa’azi aja hankalinsa. Idan yayi shikenan. Idan kuma bai yi ba, to Hukumar Musulunci tana da damar zartar da hukuncin kisa na haddi akansa.
Sallah ita ce Ginshiki mafi Qarfi kuma mafi girma daga ginshikan Musulunci. Kuma ita ce farkon abinda za’a yiwa mutun hisabi akansa aranar Alqiyamah.
Manzon Allah (saww) yace “SALLAH ITA CE GINSHIKIN ADDINI. DUK WANDA YA TSAYAR DA ITA, TO HAKIKA YA TSAYAR DA ADDINI. KUMA DUK WANDA YA RUSHETA TO HAKIKA YA RUSHE ADDINI”.
Kuma Manzon Allah (saww) yace : “Tsakanin mutum da tsakanin shirka da kafirci shine barin yin sallah”.
(Muslim ne ya ruwaito).
Kuma acikin wani hadisin, Manzon Allah (saww) yana cewa: “ALKAWARIN DA YA RABAMU DASU (WATO KAFIRAI) SHINE SALLAH. DUK WANDA YA BAR SALLAH TO YA KAFIRTA”.
(Tirmidhiy ne ya ruwaito).
(Tirmidhiy ne ya ruwaito).
Sayyiduna Buraidah (ra) ya ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa : “DUK WANDA YA BAR YIN SALLAR LA’ASAR TO LALLAI AN RUSHE AYYUKANSA”.
(Bukhariy ne ya ruwaito).
To da wadannan hadisai ne Malamai suka dogara cewar duk wanda ya dena yin sallah, to Allah ba zai karbi azuminsa ko zakkarsa ko aikin Hajjinsa ba.
Imamu Ahmad bn Hanbal yayi bayanin cewa koda mutum ba ya yin sallar ne saboda lalaci ba wai jayayya ba, to lallai duk da haka ya kafirta. Kuma Allah ba ya karbar aikin kafiri komai yawansa.
Dangane da ciwon kirji kuwa, a nemi Man Habbah da Man Shammar ko na yansun a rika hadasu ana shan cokali guda safe da rana da yamma. In sha Allah za’a samu lafiya.
WALLAHU A’ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 06-04-1438 (04-01-2017).