HUKUNCIN QIRKIRAR LABARAI
TAMBAYA TA 2082
*******************
Salamu alaikum mallam. ina fatan kana cikin koshin lafiya. tambaya na keda mallam. Mutum a facebook ya bude group da page domin kawo labarai na nishadi da labaran litaffan hausa da tatsuniyoyi da labaran ban dariya da kagagun labarai domin nishadantar da mutane da makamantansu. wasu group ma idan ka bude kayi adding members da yawa wasu har labaran batsa da hotunan batsa xakaga suna sawa. ds.
Shin miye hukuncin wanda ya bude irin wadanan group da pages din? ina bukatar mallam ya bada amsa domin nasan shima yana ganin irinsu ba iyaka. daga Aminullah Othman Alhaji.
*******************
Salamu alaikum mallam. ina fatan kana cikin koshin lafiya. tambaya na keda mallam. Mutum a facebook ya bude group da page domin kawo labarai na nishadi da labaran litaffan hausa da tatsuniyoyi da labaran ban dariya da kagagun labarai domin nishadantar da mutane da makamantansu. wasu group ma idan ka bude kayi adding members da yawa wasu har labaran batsa da hotunan batsa xakaga suna sawa. ds.
Shin miye hukuncin wanda ya bude irin wadanan group da pages din? ina bukatar mallam ya bada amsa domin nasan shima yana ganin irinsu ba iyaka. daga Aminullah Othman Alhaji.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Tabbas kusan duk mutumin dake shiga internet acikin ‘yab shekarun nan sai yaci karo da irin wadannan kirkirarrun labaran. Wasu ma babu dadin gani ballantana a karanta.
To amma Malamai sunyi sabani dangane da hukuncin kowanne irin kirkirarren labari ma.
Akwai Maluman da suke ganin cewa HARAMUN ne agun Musulmi ya kirkiri wani Qagaggen labari wanda bai faru ba. Domib yin haka yaba daga cikin Qarya. Ita kuma karya haramun ce. Allah Madaukakin Sarki ya haramta mana yin Qarya koda da wasa ne.
Kuma Manzon Allah (saww) yace : “Azaba ta tabbata bisa Mutumin da yake Kirkirar labari yake fada domin ya bama mutane dariya. Azaba ta tabbata gareshi! Azaba ta tabbata gareshi!!”.
(Abu Dawud ne ya ruwaito acikin Kitabul Adab, hadisi na 4972).
(Abu Dawud ne ya ruwaito acikin Kitabul Adab, hadisi na 4972).
Sannan acikin wani hadisin wanda Imamul Bukhariy ya ruwaito, Manzon Allah (saww) yace: “Ku nisanci Qarya domin ita Qarya tana kai mutum zuwa ga fajirci. Shi kuma Fajirci yana kaiwa mutum zuwa ga Wuta. Kuma mutum ba zai gushe yana yin Qarya kuma yana kirdadon Qarya ba, fache har sai an rubutashi awajen Allah cewa shi Makaryaci ne”.
Da kuma wani hadisin acikin Kitabul Adab na Sunanu Abi Dawud din (4782) wanda acikinsa Manzon Allah (saww) yace “Na lamunce gida agefen Aljannah ga mutumin da yake guje ma jayayya koda yana da gaskiya. Da kuma gida atsakiyar Aljannah ga mutumin da ya guji yin Qarya koda da wasa yakeyi. Da kuma gida a kololuwar Aljannah ga mutumin da ya kyautata halayensa”.
Wadannan hadisai da na lissafo, sune hujjar da Malaman suka dogara dasu cewa haramun ne Musulmi ya rika kirkirar labarai na Qarya koda da wasa ne.
A gefe guda kuma akwai Maluman dake ganin halaccin Qirkirar labari domin kaifafa hankalin al’ummah, wayar da kansu, ko kuma jan hankalinsu akan wani abu na alkhairi, ko kuma gargadinsu akan wani Mummunan abu.
Sun kafa hujjah ne da cewar akwai Malamai wadanda suka rubuta littafi na Qagaggun labarai domin nishadantarwa ko kuma Ilmantarwa. Misali kamar Maqamatul Hareeri wanda Imamul Hariri ya rubuta. Tana kunshe da Kagaggun labarai kuma har yau ba’a samu wani daga cikin Malamai wanda ya haramta ko kuma kushe abinda Malamin ya rubuta ba.
Sai dai Malaman sunce dole ne duj wani kagaggen labari ya zama bisa wadannan ka’ifodin :
1. Dole ne labarin ya zama yana karantar da wani darasi ne. Ba wai kawai don zallar dariya ba. Domin haramun ne kirkirar labarai don ayi dariya kawai. Kamar yadda hadisin chan na sama ya bayyanar.
2. Wajibi ne ya zamanto labarin ba ya kunshe da haramtattun kalmomi na shirka ko batsa, ko kuma Qaskantarwa ko wulakantarwa ga addini.
3. Wajibi ne ya zamanto babu ambaton sunayen Allah ko na Annabawa tare da yin Qarya garesu. Idan mutum yayi ma Allah Qarya, aranar lahira Mala’iku zasu nunashi agaban taron Alqiyamah suna cewa “WADANNAN SUNE SUKAYI QARYA BISA UBANGIJINSU.. HAKIKA TSINUWAR ALLAH TA TABBATA BISA AZZALUMAI”.
Idan kuma mutum ya Qirkiri Qarya ya jinginata ga Manzon Allah (saww), to lallai ya tanadar ma kansa wajen zama kenan agidan Wuta. Hakanan Qirkirar Qarya ga sauran Annabawa ma (as).
4. Wajibi ne ya zamanto basu koyar da wata haramtacciyar dabi’a kamar Bijire ma iyaye, Zina, Sata, Fasikanci, shaye-shaye, etc.
5. Wajibi ne labarin ya kunshi wani Muhimmin darasi na tarbiyyar al’ummah.
Amma duk kirkirarren labarin da ya zamanto ya sa’ba ma wadannan ka’idodin, to babu sabanin Malamai akan haramcinsa.
Duk wanda ya bude wani group ko shafi a facebook, Twitter ko Whatsapp Musamman don fitsara da ya’da labarun batsa, to hakika wannan ya chuchi kansa. Ya aikata zunubi babba. Duk wanda ya karanta, ko ya aikata wani mummunan abu ta sanadiyyar wannan shafin naka ko group, lallai kana da Kamasho mai tsoka.
Domin kuwa alhakin abun zai ci gaba da binka har bayan mutuwarka zaka ci gaba da riskar zunubai lodi lodi ta sanadiyyar wadanda zasu ci gaba da karantawa koda nan da shekaru dari ne.
Manzon Allah (saww) yace : “DUK WANDA YA SUNNANTAR DA WANI MUMMUNAN ABU, TO LODIN ZUNUBAN YANA KANSA, DA KUMA LODIN ZUNUBAN DUK WANDA YA AIKATA HAR ZUWA TASHIN ALQIYAMAH. BA ZA’A RAGE MASA KOMAI DAGA IRIN LAIFIN ZUNUNIN WANCAN DIN BA”.
Da wannan nake fatan masu bude groups ko shafi don fitsaranci ko nishadin Qarya zasu wa’azantu su tuba su dena.
WALLAHU A’ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (07-01-2017) {09-04-1438}.