Kada Ka Tsokano Fadan Da Ya fi KrfinKa Da Sunan Yaki Da Zalunci
Advertisements
FITOWA TA SHIDA (6)
Ba ya daga cikin hikima jarumta ka tsokanowa mutane fadan da ya fi karfinsu da sunan kwato musu hakkinsu. Idan kana da wata hanaya ta hikima ko ta siyasa da za ka iya amfani da ita wajen kare su daga zalunci, to sai ka yi amfani da ita. Dubi
Sayyiduna Khadir (A.S) bayan da suka hau jirgin ruwan mutanen nan miskinai, sannan aka sanar da shi cewa akwai wani azzalumin sarki a gabansu yana kwace duk wani lafiyayyen jirgin ruwa, sai ya lalalata wannan jirgin ruwan. Da haka ne ya kubutar musu da jirginsu ba tare da ya nemi fito na fito da wannan Azzalumi ba. Allah ya ba mu wannan labari inda ya ce, “Amma dangane da wannan jirgin ruwan, ya kasance na wasu miskinai ne suna aiki da shi a cikin teku, sai na yi niyyar lalata shi, kuma a gabansu akwai wani sarki yana kwace duk wani jirgi (lafiyayye)”. [Al-Kahfi, 79].