NA KASA BAMBANCE TSAKANIN JININ BARI DANA HAIHUWA, YAYA ZAN YI* ?
Advertisements
Tambaya?
Assalamu alaikum. mallan nice nake yawan yin bari( misscariage)sai wata ya kama nayi al’ada anma ba kaman yanda na saba ganin jinin al’adarba domin kuwa baizuwa da dan yawa kaman yanda nasaba ganin jinin al’ada bai wuce naganshi dis dis ba a wano toh mallam bayan kwana uku sai ya tsaya anma tundaga wan nan bansake ganin jinin ba kuma nayi gwajin ciki wanda akeyi na fitsari anma bai nunamin akwai ciki na bayan wani watan ya tsaya saina fara ganin jini shima ba yanda na saba ganin jinin al’ada ba sai ciwon ciki da mara qarni sosai gashi jajawur ga wani dan kitse da wani zare zare da yake fitowa:shin dan allah mallam ya zanyi na banbance jinin bari dana haila kasancewar nayi bari akai akai harsau 5 haihuwa 1.
*Amsa*
Wa’alaykumussalam,
Duk jinin da kika gani a BARIN da kika yi bayan ciki ya kai wata hudu, sunansa jinin haihuwa, in kuma bai kai ba sunansa jinin bari wanda baya hana sallah.
Allah ne mafi sani
*Dr Jamilu Zarewa*
21/01/2017