ALLAH NA TSARE ‘YA’YA SABODA KIRKIN MAHAIFINSU.
Idan bawa ya zama mai kirki,ya gujewa bin son zuciya,Allah yana tsare masa zurriyarsa bayan rasuwarsu ,ya tsare masa su daga sharri da tozarta.
Dubi yadda Allah ya tsare dukiyar wadannan marayu da khadir (A.S) ya mikar garu saboda dukiyarsu da take karkashinsa,don gudun kada ya fadi mutanen gari su kwashe musu dukiyarsu.
ALLAH ya ba mu labarin hakan,inda yake cewa ,”To amma dangane da wannan garun,ya kasance na wasu yarana ne marayu a cikin garin,a karkashinsa kuwa akwai wata taska tasu,mahaifinsu kuma ya kasance mutumin kirki ne,to sai ubangijinka ya nufi su kai ganiyar karfinsu, su fito da taskarsu don rahma daga ubangijinka .[Al-kahfi,82].
Advertisements