Yarda Da Kaddara A Rayuwar Mumini:!!!
Duk abubuwan da suka faru a hannun khadir (A.S) sun faru ne cikin kaddarar Allah.kuma ya nufi faruruwarsu ne domin ya sanar da bayinsa cewa yana iya kaddara wa bawa abin da ba zai yi masa dadi ba, amma bai sani ba daga karshe zai zame masa alkheri ga addininsa,kamar yadda ya faru a lamarin kashe wannan yaro ga iyayensa .ko ya zamo maslaha ne a gare shi a duniyarsa,kamar yadda ya faru a batun hudu jirgin ruwa.
wannan zai koyar da bawa hakuri da rungumar kaddarar Allah,domin fatan ta zame masa alheri a rayuwarsa ta duniya da ta addini.
Advertisements
- Dan Allah zaka iya share ga yan uwa musulmi a Facebook or whatsapp