Zul-karnain wanene?
malaman Tafsiri sunyi maganganu dayawa game da zul-karnain wanda Allah ya bamu labarinsa a cikin suratul kahfi.Dadama daga cikinsu suna cewa,shi ne Alexander dan Philip mutumin macedon ta masarautar Greek.kuma babban wazirinsa shine shaharraren malamin falsafar nan mai suna “Aristotle “.sai dai wannan magana babban kuskure ne, saboda:
1. zul-karnaini sarki ne mumini wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira. Alexander kuwa mushiriki ne mai bautar gumaka da taurari.
2. Alexander ba a kiransa da sunan “zul-karnaini”,
3. yake -yaken Alexander ba su kai kasashen Turkawa ba, iyakacinsu kasar farisa;
4. Alexander ba shi ne ya gina babbar ganuwa tsakanin Yajuju da majuju da sauran kabilu makotansu ba;
5.Alexander ya rayu ne gabanin haihuwar Annabi isah da kimanin shekaru dari uku.Yayin da zul-karnaini ya shude da dadewa
Advertisements