Dole A Samu Tarjama Domin ci-Gaban kowace Al-umma:
Domin ci-gaban kowace irin al-umma akwai bukatar a samu masu tarjama a cikin wanannan al-umma.Yana kuma daga alamun ci-bayan al-umma ya kasance a cikinta babu wadanda suka san harasan wasu al-ummomin na waje,domin karantar ilimin dake cikin wannan yaren nasu da al’adunsu ,don daukar al’adunsu masu kyau,da ci-gabansu na rayuwa.
Shi yasa Allah da ya ba mu labarin mutanen da zul-karnaini ya gina musu ganuwa a garinsu,domin kare su daga hare-haren Yajuju da Majuju , da ya tashi nuna mana koma-bayansu a rayuwa sai nuna mana basa fahimtar da yaren kowa sai nasu.
Allah yace , “Har sa da ya kai tsakanin wasu duwatsu guba biyu,sai ya samu wasu mutane kafin duwatsun biyu, da kar suke fahimtar magana.” [ Al-kahfi,93].
Allah kasa mu dace da wannan Tafseer ,Allah ka bamu ikon aikata daidai ,
Dan Allah ka yi share zuwa ga Al-ummar musulmi domin samun ladah yada alkhairi.
Advertisements