Domin Nagarta Aiki:Shugaba Ya Yi Tarayya Da Ma’aikatasa
Yana da kyau shugaba idan ya bayar da wani aiki,ya rika samun kasancewa tare da masu yi aikin,ko ya zamo mai sa ido akan aikin da ya bayar ,domin yin haka zai taimaka wajen karawa ma’aikata kuzari da karashin gudanar da aikinsu.
kamar yadda hakan na iya taimakawa musu wajen inganta aikinsu da zartar da shi yadda ya kamata.Dubi sarki zul-karnaini yadda ya kasance tare da ma’aikatansa,ya zamanto daya daga cikinsu,ana gudanar da aikin ginin ganuwa tare da shi,kuma karkashin umarninsa,kamar yadda Allah ya ba mu labarinsa inda yake cewa,zul-karnaini yace,”(ku kawo min guntattakin karafa.,”.Har sai da ya daidaita (gini) tsakanin duwatsu nan guda biyu,sai ya ce,”ku hura wuta”.Har sai da ya mayar da shi (kamar) wuta, sai ya ce,”ku kawo min narkakkiyar darma in zuba a kansa”).[Al-kahfi,96].
Allahu Akbar ,Ya Allah ka bamu ikon aikata Alkhari da kuma yan uwa su gane cewa dan ka bada aiki ka tsaya ba rashin amincewa ne ko yarda ba.
Advertisements