Ganuwar Zul-Karnaini Da Babbar Ganuwar Shina:
Akwai wasu daga cikin masana da suke da ra’ayin cewa ganuwar da Sarki Zul-Karnaini ya gina it ce babbar ganuwar nan da take kasar China. Wannan ra’ayi nasu yana da rauni sosai, saboda dalilai kamar haka:
1. Zul-Karnaini ya gina ganuwarsa ne domin raba tsakanin mutane da Yajuju da Majuju. Amma ganuwar China Sarakunan China ne suka gina ta, domin kare kasarsu daga hare-haren mayaka.
2. Ganuwar Zulkarnaini ya gina ta ne da guntattakin karafa da narkakkiyar dalma. Amma babbar ganuwar China an gina ta ne da duwarwatsu da laka.
Advertisements
3. Ganuwar Zul-Karnaini ya gina ta ne tsakanin duwatsu guda biyu, domin ya toshe hanyar da Yajuju da Majuju suke bi domin afkawa makotansu. Amma ita babbar ganuwar China an gina ta ne akan duwatsu da kwazazzabai da hanyoyi, wadda ta taso tun daga gabashin China yar zuwa yammacinta tafiyar dubunnan mila-milai.
4. Ganuwar Zul-Karnaini ba wanda zai iya fasa ta har sai wa’adin da Allah ya deba mata ya yi, wato gab da tashin kiyama. Yayin da ita kuma babbar ganuwar China ta jima da farfashewa, har mutane na shigi-da ficinsu ta samanta.
To duk wadannan dalilai ne masu nuna ganuwar da Zul-Karnaini ya gina ba ita ce babbar ganuwar China ba.