Fatawar Rabon Gado (99)
Tambaya
Assalamu alaikum malam ya za’a raba gadon wanda ya mutu ya bar ‘ya’ya maza 9 da ‘yaya mata 8 da matan aure 2 da ‘yan’uwa shakikai?
Amsa
Wa alaiku assalam Za’a raba abin da ya bari gida:8, a bawa matansa kashi (1), ragowar kashi 7 sai a bawa ‘ya’yansa Maza da mata su raba, saidai kasancewar su (26) ne, tun da kowanne namiji yana matsayin mata biyu ne, za mu buga adadinsu (26) akan asalin (8) In da zai ba mu 208, sai mu bawa matansa daya cikin (8)dinta wato (26) ta in da kowacce mace za ta samu (13), ragowar sai mu bawa ‘ya’yansa, kowanne yaro zai samu (14), kowacce yarinya kuma za ta samu (7).
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA
15/2/2017
Advertisements