Aikin Tallafi ga Dan Adam Idan Ba Allah A Ciki….
Masu gabatar da ayyukan jinkai da taimakon mabukata da agazawa gajiyayyu, ba don Allah, ba don neman yardarsa ba, sai don neman shuhura da yabo wajen mutane, da sunan taimakon jin kai ga dan Adam, wadannan ayyukansu ba su da wani rabo na lada a wajen Allah. Sai wanda ya yi aikinsa yana mai imani da Allah, kuma yana neman sakamako a wajesa shi ne Allah zai biya shi ranar gobe kiyama.
Akwai wani babban mai arziki a zamanin jahiliyya da ya shahara da taikon talakawa da gajiyayyu, don taimakawa baki da matafiya, amma bai yi imani da ranar lahira ba. Sai wata rana Sayyidatuna A’isha ta cewa Manzon Allah (S.A.W) “Ya Ma’aikin Allah, Abdullahi bn Jud’an a zamanin Jahilayya ya kasance mutum ne mai girmama baki da sada zumunci da fansar bayi, tare da kyautatawa makota”. Ta yaba masa sosai, sannan ta ce, “Shin hakan zai amfane shi a gurin Allah?”.
Sai Mazon Allah ya ce, “A’a! Saboda bai taba budar bakinsa ya ce, ‘Allah ka gafarta mani kurakuraina ba ranar gobe kiyama’ ”.[ Ahmad, 2489.
Ku kasance da sadeeqmedia.com.ng domin samin karance -karance da karatutuka na Addinin musulunci
Advertisements