Dan Aljannah Ba Ya Bukatar Wani Canji:
Allah da ya halicci dan Adam ya kuma saukar da shi a doron kasa, sai ya kimsa masa sha’awar samun canje-canje na yanayi da guri da hali. Yayin da ya dade a cikin wani yanayi ko guri daya, duk yakan ji ya gundure shi, ya gaji da shi, komai dadinsa, yana son ya ga wani canji. Wannan yanyin halitta da Allah ya yi wa dan Adam, ita ce take taimakon shi wajen kawo ci-gaba a rayuwa ta duniya, da raya kasa, da habaka ta, kamar yadda Allah ya nema daga wajensa.
Amma a Aljanna sai Allah ya cirewa masa wannan sha’awar, ya sanya masa tsananin kauna da sha’awar zama guri guda, ba tare da ya kosa ba, ko ya rika tunanin canji daga yanayin da yake ciki na ni’ima zuwa wani yanayi daban. Wannan kuma shi ne ya fi dacewa da rayuwar dan Aljanna wanda Allah ya masa tanadin duk wata bukatarsa, ya samar masa duk wani abu na jin dadi da morewa a cikin gidan Aljannah.
Da a ce, za a bar shi da waccan sha’awa ta shi, kamar yadda take a duniya, to da ya nemi Allah ya canza masa wata aljannar ba wadda yake ciki ba, domin ya gaji da ita. Shi ya sa Allah ya ce mana, “Lallai wandanda suka yi imani kuma suka yi aiki na kwarai, ajannatan Firdausi sun tabbata masauki gare su. Suna masu dawwama a cikinsu, ba su bukatar wani canji game da su”. [Al-Kahfi, 107-108].
Allah Kasa mu shiga Aljannah don Rahamarsa.
ku kasance da sadeeqmedia blog domin samun,Fatawa,Tafseer,Wa’azi da sauransu
Advertisements