Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home ยป Kungiyar Izala Zata Zagaya Jihohin 37 Harda Abuja A Tarayyar Nigeria
ISLAM

Kungiyar Izala Zata Zagaya Jihohin 37 Harda Abuja A Tarayyar Nigeria

iGeekBy iGeekMarch 12, 2017No Comments1 Min Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Kungiyar Izala zata zagaya jihohi 37 harda Abuja a tarayyar Naijeriya 

Daga: Ibrahim Baba Suleiman 

A ranar alhamis dinnan mai zuwa (16/3/2017 (wato 17/6/1438AH) in sha Allah. Kungiyar Izala zata fara zagaye zuwa wajen ‘ya’yanta a jihohi 37 harda Abuja da ke fadin kasar Naijeriya

Shugaban kungiyar ta tarayyar Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya shaidawa manema labarai cewa, kungiyar zata zagaya zuwa jihohin ne domin ganin yadda ayyukan kungiyar suke tafiya a lungu da sako tare da wasu birane na sassan kasar.

Zagayen wanda za’a fara da jihohin Bauchi, Gombe, Adamawa da taraba, Manufar zagayen shine ‘Karantar da masu wa’azi’ domin inganta harkokin Da’awa zuwa ga wadanda basu fahimci addinin islama ba, tare da farfado da harkokin ilimi a makarantun Islamiyya da dai sauran su.

Jadawalin zagayen na farko zai kasance kamar haka;
Kwana daya aka kebewa kowace jiha. 

Jihohin farko sune-
Bauchi 16/3/2017, 
Gombe 17/3/2017,
Adamawa 18/3/2017 
Taraba 19/3/2017. 

Tawagar da zasu raka Shugaba Sheikh Bala Lau ta hada da wasu shugabanni, Malamai da daraktocin kungiyar a matakin kasa,  zata sauka a birnin Bauchi da misalin karfe 12 na ranar Alhamis 16/3/2017 in sha Allah.

Sanarwa daga ofishin babban sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe.

#Jibwis_Nigeria
13/Jumada Awwal/1438
12/March/2017

Advertisements

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Wa'azin IZALA a kasashen Turai Da Lokutan Da Zasuyi Wa'azi a ko wace Kasa Kamar Yadda Wannnan Hotunan Ya Nuna

November 25, 2017

Darikar Tajjaniyya Da Shi'a Duk Daya Ne, Cewar Sheik Dahiru Bauchi

June 20, 2017

Bajintarsa A Gasar Kur'ani Ta Sa Limamin Harami Ya Sumbace Shi Daga Abu Abdur

June 14, 2017
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.