Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home » Halima Atete Dalilan Da Sukasa Naki Yarda A Askemun Gashin Kaina Domin Daukar Film Din Sultana.
kannywood

Halima Atete Dalilan Da Sukasa Naki Yarda A Askemun Gashin Kaina Domin Daukar Film Din Sultana.

iGeekBy iGeekApril 4, 2017No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email
Halima Atete Dalilan Da Sukasa Naki Yarda A Askemun Gashin Kaina Domin Daukar Film Din Sultana.
Daga : Sani Adamu Chirome.

Halima Atete tana daga jerin jarumai mata wanda duk irin matsayin da kace su fito zata iya fitowa. Tana fitowa amatsayin masifaffiya misali cikin fim din “Dakin Amarya” sannan tana fitowa amatsayin mai barkwanci misali cikin fim din ” Mata Maza” tana fitowa matsayin soja misali cikin fim din “Auren Soja”.

To abinda yaba sauran daraktoci mamaki shine kin yarda da ta fito cikin wani sabon fim na mawaki Nura M Inuwa maisuna “SULTANA”. Jarumar ta fadi dalilan da suka hana ta fitowa acikin fim din Sultana. Acewarta:
Ni dai bazan iya fitowa amatsayin jarumar cikin fim din ” Sultana” ba.

Sabida dalilai masu tarin yawa. Dalili na farko shine labarin fim din ya nuna cewa dole sai an aske gashin duk jarumar da zata fito acikin fim din.
Ni kuma gaskiya bazan yarda da haka ba. Domin ya sabawa addinin Islama kuma Allah ya tsinewa duk macen da ta aikata haka.

Na biyu, na tambayi iyayena shawara akan haka amma sunce idan na aikata haka to tabbas tsinuwar Allah da tasu zata tabbata akaina. Ni kuma duk abinda iyayena sukace kada nayi to Wallahi ko nawa zan samu bazan yi shi ba. Ko wannan fim da nakeyi sai da suka amince sannan na fara yi.
Na uku, gani nayi mutuncin mace da kwarjina shine kamin kanta. Idan na aske gashin kaina to zan sami kudi amma kuma zan rasa mutuncina a idanun duniya.

Masoyana ba zasu yi farin ciki ba idan na aske gashin kaina.
Na hudu, samarina zan daina burgesu da dogayen gashin kaina. Duk da nasan wani gashin zai fito amma kafin ya fito nasha bakin ciki mara iyaka.

Sannan ni bance Nafisa da ta fito acikin fim din Sultana ta aikata laifi ba. Ra’ayinta ne yasa ta fito, ni kuma maganar Allah ce ta hana ni na fito, amatsayin wadda za’a askewa gashin kanta.

African Actress /Kannywood || Producer || FB: Facebook.com/haleemaatete || Twitter: @haleemaatete.
Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Yadda wasu fitattun jaruman sunka kwashe shekaru cikin masana’atar fim

January 30, 2023

Hirar murya kunya yar tiktok a hannun yan sanda

January 30, 2023

Karshen Tika Tik : Lilin Baba Ya Bayyana Hotunan Yaronsa Na Farko

January 10, 2023
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.