Close Menu
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
  • Home
  • E News
  • Bollywood
  • Hausa series
  • kannywood
  • Tech
Facebook X (Twitter) Instagram
Hausaloaded
Home ยป Man Utd za ta girmama 'yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria
SPORT:::::::::::::

Man Utd za ta girmama 'yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria

iGeekBy iGeekApril 28, 2017No Comments2 Mins Read
Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
Share
Facebook Twitter LinkedIn Pinterest Email

Man Utd za ta girmama ‘yan kallon da lantarki ya kashe Nigeria

Kungiyar kwallo kafar Manchester United ta ce za ta girmama magoya bayanta da suka mutu bayan turken wutar lantarki ya fada kansu a lokacin da suke kallon wasa a birnin Calabar na jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, United ta ce ‘yan wasanta za su daura wani bakin kyalle a hannayensu a wasan da za su yi ranar Lahadi “domin tunawa da magoya bayanmu bakwai da suka mutu a kwanakin baya a Calabar da ke Nigeria.”
Hukumomi sun ce mutum bakwai ne suka mutu a lokacin da lamarin ya faru, yayin da wasu goma suka samu raunuka.
Sai dai wasu da suka shaida lamarin, sun fada wa BBC cewa adadin ya fi haka, yayin da kafafen yada labarai na cikin gida ke cewa mutum 30 ne suka mutu.

Lamarin ya faru lokacin da jama’a suka taru suna kallon wasan Europa tsakanin Manchester United da Anderletch.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya “kadu kwarai” da jin labarin abin da ya faru wanda ya janyo asarar rayuka.

Rahotanni sun ce gidan kallon ya cika makil da mutane a lokacin da babban layin wutar ya katse, inda ya fado kan jama’a.

Advertisements

Share. Facebook Twitter Pinterest LinkedIn Tumblr Email
iGeek
  • Website

Related Posts

Sevilla Ta Karya Tarihin Shekara (60) Na Manchester United

March 16, 2018

Real Madrid Sun Shiga Sahun Mahaukata Akan De Gea – Mourinho

March 16, 2018

Ina So Allah Ya Hadamu Da Liverpool ko Real Madrid – Dzeko

March 16, 2018
Leave A Reply Cancel Reply

Recent Comments
  • fbdownloader on Download Nura M Inuwa Full Wedding video part 3 2017
  • Muhammad on MUSIC : Umar M Shareef – Tsohuwata Zuma
  • Unknown on MUSIC : sayyad Gadon Kaya – Shakuwa A So
  • Abubakar Rabiu on [MTN]Yadda Zaka Samu Free 1GB Data A Layin Mtn
  • IBRAHIM BELLO GIDADO on Lastest song Rarara again TALEKO TA LABE MP3
Facebook X (Twitter) Instagram Pinterest
  • About Us
  • Contact Us
  • Disclaimer
  • Privacy Policy
© 2025 ThemeSphere. Designed by ThemeSphere.

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.